Labarai

Yadda Sadiya Haruna ta rasa inda zata saka kanta don murna lokacin da aka saki besty kanin ta

Yadda Sadiya Haruna ta rasa inda zata saka kanta don murna lokacin da aka saki besty kanin ta

Kamar yadda kuka sani bayan kwana biyu da suka gabata ne aka dauke kamin Sadiya Haruna mai suna Umar, inda Sadiya Haruna ta bayyana a cikin wata bidiyo wanda ta wallafa shafin ta na sada zumunta instagram tana kuka.

Bayan wannan lokacin sai aka saki kanin nata amma sai aka sake kama daya kanin nata shi kuma mai suna besty, wanda hakan ya kara daga hankalin Sadiya Haruna wanda har tayi barazanar cewa sai tayi karar duk mutanen da suke takurawa rayuwar ta.

To a yau kuma Sadiya Haruna ta wallafa wata bidiyo a shafin ta na sada zumunta instagram inda muka ga Sadiya Haruna tana murna sabida an saki kanin nata mai suna besty.

Tsananin jin dadi da farin ciki har yasa Sadiya Haruna ta rasa inda zata saka kanta inda ta rungumi kanin nata tana murnar dawowar sa.

Zaku iya kallon bidiyon dake kasa domin kuga irin murnar da Sadiya Haruna tayi a lokacin da aka saki besty kanin ta ya dawo gida.

Ga bidiyon nan a kasa domin ku kalla kai tsaye.

https://www.instagram.com/tv/CZcf397qwsG/?utm_medium=copy_link

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button